• Sat. Jul 20th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Yadda Zaki Dawo Da Ni’imarki Bayan Kin Haihu

Da yawa daga cikin magudanta maza suna korafi na rashin jin dadin matansu daga lokacin da suka haihu. Hakan ne yasa amihad.com tayi bincike kan wannan lamari domin kawo muku mafita akan wannan matsala.

Akwai lokacin daya kamata uwargida ta fara wannan shiri bayan ta haihu domin abu bana lokaci guda ba ana yinsa ne har sai an samu mafita. Dan haka zamuyi bayani daki-daki.

BAYAN SATI BIYU DA HAIHUWARKI

IDAN KIN HAIHU sai ki Fara shirya jikinki don tarbar maigida, don in dai lafiya kika haihu Daga lokacin Zaki tsinci kanki cikin kuzari. Duk wanda ya ganki zai ganki tas kamar ba ki haihu ba.

Don haka tunda tafiyar ta samu sai a Fara shirya jiki, Kiyi kokarin a dafa miki kaza irin ta masu jego ki Fara ci, (Inda babu kada ki matsawa mijinki ) cin kazar yana Kara gyaran kasan mace maigida yaji ta zam- zam kamar bata haihu ba.

  1. Shan ya’yan itatuwa akai-akai baran ma (kankana, abarba, gwada, lemon zaki).
  2. Ki dinga yin Kunun aya kina sha. In zai samu Kiyi kullum, amma karki dinga zuba sukari dan kadan zaki dinga sawa ko ki sha haka.
  3. Shan maganin Mata mai kyau (habbatus-sauda, Zuma, dabino, aya ,madara, nono amma me kyau.
  4. Shan Zuma madi, tsimi da saurabsu.
  5. Tun Daga ranar da kika haihu har zuwa lokacin da zaki yi arba’ in ki zama cikin tsaftace jiki da gyaran jiki , gyaran jariri, gyaran gida.

KUMA KARKI YI SAKE DA YIN TURAREN WUTA DANA JIKI DA GIDANKI DA JIKINKI

Don wasu matan idan suka haihu sai kaganta (ragajab ba tsaftace jiki) ko ina su a ganin su idan Ana jego ba a gyaran jiki tunda mijinta Baya tare da su a shimfida, kana zuwa kusa dasu sai kaji wari da karni, wanda a musulinci ko yau mace ta haihu jini ya dauke Mata a ranar data haihu, mijinta yana da ikon zuwa ya sadu da ita a Rana.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *