• Sun. Nov 10th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Yadda Zaki Shawo Kan Matsalar Mijin Da Baya Baki Hakkin Ki

ByLucky Murakami

Aug 17, 2022
Yadda ake jawo hankalin maza

Matsalar zamantakewa matsala ce wadda babu mai iya maganin ta sai Allah musamman idan har Ma’auratan Basu sa tsoron Allah a Rayuwar su da kuma hakuri.

Shi hakuri a kowa wane bangare na rayuwar mu yana da mahimmanci, dan haka ya kamata musan mahimmancin sa a auratayya. Muddin kikayi hakuri toh wallahi duk wata matsala mai sauki ce.

Abunda nake so mu kula game da matsalar Mijin da baya cika hakkokansa akan ci shine, shin wane irin hakkin ne baya cika wa, sannan kuma ke wane irin kokari kike yi dan ganin kin maganace irin matsalar.

A gaskiyar magana mafi yawan cin maza suna bawa mata hakkin su na Aure musamman idan muka duba cewa wasu suna kokarin yi dai dai karfin su.

Amma wasu matan muna so muga mazan mu sun yi mana abu yadda muakaga mazan wasu suna musu.

Ya mata ki fahimci cewa kowa da irin karfin da Allah ya bashi, idan duk abunda Allah ya hore wa mijinki to kiyi hakuri dashi kuma kiyi wa Allah godiya sannan shima mijin ki yawaita masa godiya akan duk irin abunda ya kawo mishi.

Hakan zaisa Allah ya saka miki natsuwa a rayuwarki sannan ya cire miki damu.

Babban maganin matsalar Mijin da baya ba macce hakkin ta shine ki tashi tsaye ki fara sana’a domin duk wani abu da ya shafi kudi zaki iya daukar nauyin sa ba tare da wani bacin rai ba.

Wani lokacin kina shaawar ki mallaki wata sutura amma mijin baida hali ko kuma yana kokarin ganin ya kawo abinci gida kinga hakan zaisa ki mallaki wannan suturar ba tare da ya baki kudi ba.

Dan haka ki nema Izini wajen sa ki fara sana’a idan Allah ya sanya wa Sana’ar albarka zaki ga kina daukar nauyin kanki a wasu abubuwa da dama ba tare da ya sani ba musamman abunda ya shafi bukin kawaye ko na gidan ku.

Akwai matsalar hakkin mata da ke kan miji da bai shafi kudi ba, misali ta saduwar Aure.

Yana da kyau ace tun farkon auren ku ki fahimci mijinki wace irin mace yafi shaa’awa sannan kiyi kokari ki zama irin wannan macen. Saboda a duk lokacin da mijinki ya ganki zaiji shaawar ki.

Wasu matan aure basu kula da wannan kuma yana daga cikin manya manyan dalilin da zai sa mijinki yaji baya shaawar saduwa dake domin kuwa kowane namiji yana da irin abunda ke tada mishi shaawa a jikin mace.

Tilas ne kisan me ke tawa mijin ki shaawa domin hakan zai rika sa ya kusance ki.

Muddin baki kula da wannan ba to ki tabbatar da dole matan waje su rika ba mijin ki shaawa, wanda zai iya kai shi ga auren wata mata ko neman matan banza a waje.

Allah sa mu gane gaskiya ya bamu ikon binta.

Amma duk wata da take fuskantar matsalar namijin da bayan kula da hakkin ta to tayi kokari ta tabbatar da ba laifin ta bane kuma idan abun ya ci gaba a sanar da maganbata kada ki bari irin wannan matsalar ta jefa ki cikin sabon Allah.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

One thought on “Yadda Zaki Shawo Kan Matsalar Mijin Da Baya Baki Hakkin Ki”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *