Close Menu
    AMIHAD.COM
    • Admission
    • Education
    • Finance
    • Scholarship
    • Tech
    • Visa
    AMIHAD.COM
    Kannywood

    Yanzu Yanzu Ana Neman Safara’u Da Mr 442 Ruwa A Jallo

    Lucky MurakamiBy Lucky MurakamiAugust 24, 2022Updated:August 25, 2022No Comments2 Mins Read

    Kamar yadda mutane da dama suke mika kokensu lokuta da dama akan ya kamata hukuma tayi wani abu akan lamarin wadannan matasan mawaka.

    Hakan yasa wasu har bidiyo sukai domin nuna rashin jin dadinsu na hadakar wadannan matasan mawaka wanda wasu suke cewa bai kamata Mr 442 da abokanansa su dauki yarinya karama kamar Safara’u su ajiyeta a dakin otal suna aikin waka tara.

    Wanda wasu mutane sunyi kokarin yiwa iyayen ita wannan yarinya SAFA da su duba lamuran yarinyar nan sannan su kuma Mr 442 da sauran wanda suke tare akayi ta musu nasiha da suji tsoron Allah.

    Bai kamata ace sun dauki yarinya karama tabar gidan iyayenta hakan ya sabawa shari’a wanda wasu suke bada misali na cewa ai suma suna da kanne, shin zasu so suga anyi ma nasu haka?.

    Idan baku manta ba shafin amihad.com a baya ya kawo muku yadda Wata Uwa Ta Gari Ta Yiwa Safa Safara’u Nasiha Akan Abinda Take.

    Sai dai kuma labarin da muke samu a yammacin yau tabbas ya dauki hankalin mutane inda muka samu sanarwa kamar yadda zamu gabatar muku a kasa.

    Muna Neman Safara’u Da Mr 442 Ruwa A Jallo, Cewar Shugaban Hukumar Tace Finafinai Na Jihar Kano.

    Labarin da muka samu shine a wata tattaunawa da shugaban hukumar tace finafinai na jihar Kano, Isma’il Na’abba Afakallu yayi da majiyarmu, jaridar SARAUNIYA NEWS ya bayyana cewar, yanzu haka neman Safara’u suke yi ruwa a jallo ita da mawaƙi Mr 442.

    Ya ƙara da cewa yanzu haka sun arce sun yi ƙaura daga jihar Kano, domin dokar jihar ba za ta ba su damar yin abinda suke so na ɓata tarbiyya ba.

    Hakika wannan labari ya sanya mutane maida martani iri-iri akan faruwar wannan lamari sai dai kuma wasu suna cewa maganar a kama wadannan mawaka bata taso ba.

    Shin me zaku ce akan faruwar wannan lamarin?

    Related Posts

    Shin Dagaske Ne Jaruma Fati Washa Tafi Duk Matan Kannywood Kyau?

    November 24, 2022

    Jaruman Kannywood Sun Jawowa Kansu Magana Saboda Wannan Bidiyo Da Sukayi

    November 20, 2022

    Kalli Bidiyon Maryam Yahaya Tana Rawar Yan Kauye Kafin Ta Shiga Harkar Fim

    November 18, 2022

    Junaidiyya Gidan Badamasi Ta Bayyana Dalilin Dayasa Ta Fito Daga Gidan Mijinta Ta Fara Harkar Fim

    November 18, 2022

    Jerin Matan Da Adam A Zango Yayi Soyayya Dasu A Kannywood

    November 18, 2022

    Kalli Abinda Hamisu Breaker Da Momee Gombe Sukayi A Gidan Gala Wanda Ya Jawo Musu Magana

    November 16, 2022
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    • About Us
    • Contact Us
    • Disclaimer
    • Privacy Policy
    • Terms & Conditions
    Copyright © 2025 AMIHAD.COM | All Right Reserved.

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.