• Sun. Dec 8th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Yaudara Kala Uku Da Maza Ke Yiwa Mata A Wannan Zamanin

ByLucky Murakami

Mar 7, 2024

YAUDARA IRI UKU DA MAZA SUKE YIWA MATA

Duk wata mace a rayuwa matukar ta kai munzalin girma Kyakkyawa ce ko akasi ba ta rasa masoyi wanda zai ce yana sonta, musamman a lokacin girma kamar 16-17-18- 20 22.

Kuma a wannan lokacin ya’ya mata sunfi farin jini, shiyasa duk wata mace da ta tsaya ruwan ido ba tayi zaɓi ba a wancan lokacin takan yi nadama.

Shawara ga kowacce mace ta yarda da kaddarar ta ta zaɓi mutumin kirki ta cire son abin duniya matukar akwai sana’a da halayya yana sallah lokaci biyar.

Mace musamman budurwa kar ta yarda ta yi soyayya da wanda bai nemi iznin iyayen ta ba, ko wai hira sai dai su tafi wani wuri ko sai a makaranta da dai sauran su.

1. Saboda Burgewa

Wani namiji zai ce yana son mace ne saboda kawai tana burge sa, shi ba yi ma da burin aure yanzu sai dai kawai ayi ta soyayya a bata wa juna lokaci

Wannan irin soyayyar kada ki yarda da shi ki kame kanki ki fuskanci karatun ki in kina wata sana’a shima ki fuskanta domin irin wannan soyayyar sau da dama mazan ba sa gayawa mata gaskiya ke ga ki kina ta zaton zai aure ki amma shi kawai yana tare da ke ne don ebe kewa waya chatting dss, amma ba ya kaiki ga sabon ALLAH.

2. Saboda Son Abun Duniya

Wanda kawai shi don gidan ku akwai dukiya ko sarauta don ace yana soyayya dake abin alfahari ne ko don kwadayin irin kina kashe masa kudi da dai sauransu, amma ba don auren ki ba.

3. Saboda Sha’awa

Shine mafi munin yaudara wanda zai nuna miki matukar so da salo iri iri amma shi daman kawai burin sa sha’awa kike ba shi, ya yaudare ki ya ta’ka ki wato yayi zina dake, irin su sukan kasance mayaudara masu salo salo.

Shiyasa duk wani namiji musamman ke BUDURWA da ya fara kawo miki maganar banza ki fita daga harkar sa na har abada, duk irin soyayyar da kike masa duk tsanani da za ki shiga mai sauki ne akan wanda za ki shiga in kika saɓawa ALLAH da shi.

Rabuwa dai daman dole ku rabu shi irin wannan namijin daman ba auren ki bane a gaban sa, kuma wulakanci da tozarci ne zai biyo bayan yarda da shi.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *