Hakika rayuwar yau ta koma abinda kake dashi shine mutuncinka domin duk lokacin da akace bakadashi to zakaga wulakanci kala kala.
Rahoton d muka samu daga jaridar Premium Times ta bayyana cewa wani dan kasar Honduras mazaunin kasar Amurka mai suna Danny Gonzalez ya karyata mutuwarsa domin guje wa yawan bani-bani daga wurin matar sa.
Gonzalez na daya daga cikin ‘yan kasar Honduras da iyalen su ke dogaro da su sanadiyyar zaman da suke yi a can kasar Amurka.
Gonzalez ya ce tun da ya koma zama a kasar Amurka matar sa ta zama aljihu da kulum sai dai a zuba masa kudi.
Ya ce “Duk ranar Asabar matata kan kira ni a waya sannan duk kiran da za ta yi mun na tambayar kudi ne daga nan kuma babu abin da zai sake hada ni da ita.
“Ganin yawan bani-bani din da matata ke yi ya ishe ni sai na dauki wannan mataki na in karyata mutuwa ta.
Ai ko bayan ya aika mata da hotunan sa kwance kamar gawa, sai ko ‘yan uwansa suka rude, suka fara neman yadda za suyi su tabbatar da haka. Jaridu suma basu bar maganar ta wuce haka kawai ba.
Daga baya sai aka gano cewa ashe bai mutu ba yana nan da ran sa lafiya sumul. Matar sa ce kawai ya nemi ya tada wa hankali ko ya huta da tambaya.
Asirin Mata Masu Nuna Tsiraicinsu Ga Yan Uwansu Mata Ya Fara Tonuwa
Munyi karo da bayani na ilimi akan hukuncin mata masu nuna tsiraicinsu ga yan uwansu mata da tunanin hakan ba komai bane. Saiku gyara zama domin karanta cikakken bayani.
Mace ta ba da jikinta ga mata ‘yan’uwanta don a yi mata wanka saboda kwalliya ko irin dilka da halawa din nan wai haramun ne?
Ko da ta rufe mamanta da mazaunanta?
In haramun ne kenan daga ina zuwa ina ne tsiraicin mace da bai kamata ‘yar’uwarta mace ta gani ba? Jazakallahu khairaljazaa.
To ‘yar’uwa malamai sun yi sabani game da tsaraicin mace ga ‘yar’uwarta musulma, akwai wadanda suka tafi a kan cewa: bai halatta ‘yar’uwarta mace ta ga wani abu a jikinta ba, sai abin da ya saba bayyana a tsakanin mata, idan suna zaune i-su-i-su, kamar kafa da hannu da fuska da wuya da makamacin haka.
Sai dai abin da mafi yawan malaman fikhu suka tafi a kai shi ne: al’aurar mace ga.
‘Yar’uwarta musulma tana farawa ne daga cibiya zuwa guiwa, kamar yadda al’aurar maza take a tsakaninsu.
Don haka bai halatta ta bari wata mace ta kalli sama da wannan wurin da aka iyakance ba, amma idan kafira ce matar to malamai sun yi bayani cewa ba za ta kalli wani abu ba, sai abin da ya saba bayyana, don haka sai a kula lokacin da za a je dilka wajan wacce ba musulma ba, don kada garin neman gira a rasa ido.
Sannan a bisa wannan bayanin da kika yi, dilkar da kika siffanta za ta zama ba ta halatta ba, tun da za a ga abin da shari’a ba ta halatta a gani ba.
Allah ne mafi sani.