Kamar yadda muka samu labari an dauki Fatima zuwa Abuja don sake yanke mata kafa a karo na biyu bayan wancan aiki na farko da akayi mata likitoci sunce ba’a gama yankewa ba.
Da farko dai an samu jita jitar cewa Sarki Ali Nuhu ya bada kyautar Naira miliyan biyu wa Fatima wacce aka yankewa kafa.
Har ake cewa babu shakka jarumi Ali Nuhu yayi wani abu wanda duk wani mutum na kwarai zai saka masa albarka ya kuma gode masa da ana zargin Ali Nuhu a matsayin wanda baya kyauta ko sadaka ashe shi idan ya tashi yi babu wanda yake sani sai yanzu da abu yayi yawa kuma zamani ya chanja indai yayi abun arziki Bama ya sanin mutane sun sani kawai sai dai yaji a gari.
Fatima tana cigaba da haduwa da jarabawa bayanda mumunar kariyar da samu a kafarta sanadiyar tukin ganganci da wani matashi yayi a sokoto.
Bayan Kai Fatima asibiti da Yanke kafar a yanzu haka Fatima na fama da jarabobi guda ukku da suke naiman agajin gaggawa, Fatima na fama da shari’a,rashinkudi da fuskantar kara yankewar kafarta saboda kwayoyin cuta da sukeci gaba da mamaye kafarta saboda rashin yimata igantaccen aiki.
Sai gashi wata sanarwar da take kara fitowa da zafi zafi ta cewa za’a yanke mata daya kafar yanzu dai subhanah zata kasance bata da kafa ko daya kenan wannan dai abu baiyi dadiba kuma abun dole ka tausaya wa wannan yarinyar da irin wannan kaddarar data sameta.
Ga dai bidiyon da muka samo wannan rahoto a kasa sai ku kalla don jin cikaken bayani.
https://www.youtube.com/watch?v=wDezI7B-WNc
Yanzu haka Fatima na Abuja kwance a asibiti ana kokarin sake Yanke Wani bangaren kafar da tasamu kariyar saboda rashin igantaccen aiki da akayi mata daga asibitin garin sokoto.
Yanzu haka dai fatima sun asibiti abuja domin kara duba lafiyarta wannan yayi sanadiyar za’a kara gunci kafar daga inda anka yanka a nan Sokoto wanda a cikin wannan bidiyo zaka fahimci fatima tana cikin mummunan hali tare da ban tausayi sosai.
Fatima tana neman taimako mutane duba yadda sunkaje kotu amma sai labari ya chanza na rashin halarta alkali kotu tare da hana manema labarai daukar rahoto a wajen wanda ya nuna cewa Fatima bazata samu adalci a wannan kotu ba duba da yaron dan wasu sune.