Zan Iya Sadaukar Da Kafa Ta Daya Ga Fatima, Cewar Ibrahim Abubakar Funtua
“Da likitoci za su tabbatar min da cewa idan aka cire kafata daya za ta iya yi wa Fatima wadda ta rasa kafarta a Sokoto, Wallahi da na ba ta. Amma ina sauraren karin bayani daga kwararrun likitoci”, cewar Ibrahim Funtua.
Fatima tana neman taimako mutane duba yadda sunkaje kotu amma sai labari ya chanza na rashin halarta alkali kotu tare da hana manema labarai daukar rahoto a wajen wanda ya nuna cewa Fatima bazata samu adalci a wannan kotu ba duba da yaron dan wasu sune.
Fatima tana cigaba da haduwa da jarabawa bayanda mumunar kariyar da samu a kafarta sanadiyar tukin ganganci da wani matashi yayi a sokoto.
Bayan Kai Fatima asibiti da Yanke kafar a yanzu haka Fatima na fama da jarabobi guda ukku da suke naiman agajin gaggawa, Fatima na fama da shari’a,rashinkudi da fuskantar kara yankewar kafarta saboda kwayoyin cuta da sukeci gaba da mamaye kafarta saboda rashin yimata igantaccen aiki.
Sai gashi wata sanarwar da take kara fitowa da zafi zafi ta cewa za’a yanke mata daya kafar yanzu dai subhanah zata kasance bata da kafa ko daya kenan wannan dai abu baiyi dadiba kuma abun dole ka tausaya wa wannan yarinyar da irin wannan kaddarar data sameta.