Close Menu
    AMIHAD.COM
    • Admission
    • Education
    • Finance
    • Scholarship
    • Tech
    • Visa
    AMIHAD.COM
    News

    Yadda Aka Kama Dalibai Mata 4 Suna Madigo a Cikin Daki

    Lucky MurakamiBy Lucky MurakamiOctober 27, 2022No Comments1 Min Read

    Kwallejin Kimiyya da Fasaha na Jihar Kebbi da ke Jega ta kori wasu dalibanta mata hudu saboda samunsu da aikata laifin madigo.

    Daily Trust ta ruwaito cewa shugaban makarantar da aka yi wa karin daraja, Aminu Dakingari, ya ce jami’an tsaro da masu sharar dakunnan kwanan matan ne suka kama ‘yan matan yayin da suka aikata madigon.

    Ya ce an kafa kwamitin ladabtarwa wadda ta gudanar da bincike kan lamarin kuma ta gano daliban sun aikata laifin kana daga bisani aka kore su daga makarantar.

    “Daliban sun fadawa kwamitin binciken cewa sun aikata laifin saboda haka ya zama dole mu kore su daga makarantar,” inji shi.

    Ya kara da cewa daliban sun rika masa barazana bayan an kore su daga makarantar, “Sun rika barazanar halaka ni ta hanyar sakon tes amma hukumomin tsaro sun shiga tsakanin mu,” a cewar shugaban makarantar.

    Ya kara bayani inda ya ce biyu daga cikin daliban da aka kora ‘yan garin Kontagora ne a jihar Neja yayin da sauran biyu sun fito ne daga jihohin Kebbi da Sokoto. Madigo da luwadi dai manyan laifuka na a dokar Najeriya.

    Related Posts

    Tofah Bayan Ganin Bidiyon Tinubu Yana Motsa Jiki, Malmai Sun Fara Zazzago Martani

    January 11, 2024

    Yadda Wata Matar Aure Ta Kama Mijinta Yana Cin Amanarta Ba Kunya Ba Tsoron Allah

    December 25, 2022

    Karshen Duniya Yazo: Yadda Dalibi Ya Dirkawa Malamarsa Ciki

    December 12, 2022

    Wani Dalibi Ya Kashe Kansa Saboda Ya Kasa Mallakar Wayar Naira Dubu Hamsin

    November 27, 2022

    An Kama Likitan Bogi Daya Dirkawa Yan Mata Hudu Ciki

    November 26, 2022

    Yadda Mahaifiyar Budurwa Tasa Saurayi Ya Dirkawa ‘Yarta Ciki

    November 25, 2022
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    • About Us
    • Contact Us
    • Disclaimer
    • Privacy Policy
    • Terms & Conditions
    Copyright © 2025 AMIHAD.COM | All Right Reserved.

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.