Close Menu
    AMIHAD.COM
    • Admission
    • Education
    • Finance
    • Scholarship
    • Tech
    • Visa
    AMIHAD.COM
    Family & Relationships

    Yadda Amarya Ta Mutu Ranar Daurin Aurenta

    Lucky MurakamiBy Lucky MurakamiOctober 29, 2022No Comments1 Min Read

    Wata Amarya mai suna Hannatu Yahaya, ta rasu ranar da aka daura mata aure. An daura wa Hannatu aure tare da Isyaka Yusuf, a Kawon Maigari da ke Kano, ranar Juma’a 28 ga watan Oktoba, amma sai ta mutu a wannan ranar a Kano.

    Yan uwanta sun ce bayan an daura aurenta, lokacin da aka shirya domin a kai ta gidan mijinta, sai Hannatu ta fara yin ababe masu ban mamaki. Ya ce ta fara lalata kayakin gidansu tare da fizge-fizge har sai da aka kamata aka rike.

    Daga bisani an kai ta Asibiti inda aka tabbatar da mutuwarta.

    Kazalika wani dan uwanta ya ce, mako biyu da suka gabata, hannatu ta yi fama da cutar gyambon ciki wato ulcer, kuma sakamakon haka aka kwantar da ita a asibiti har tsawon mako daya. An sallameta ranar Alhamis 25 ga watan Nuwamba daga Asibiti.

    Ya ce ta sake kamuwa da rashin lafiya kuma, amma ta sha magunguna. Ya ce lamarin jikinta ya rikice ne ranar da aka daura aurenta, kuma lokacin da ake kokarin kai ta gidan mijinta.

    Allah ya jikanta.

    Related Posts

    Yadda Kanin Miji Ya Dirkawa Amaryar Yayansa Ciki A Nasarawa

    November 19, 2022

    Sati Biyu Kacal Da Yin Aure Amarya Ta Bukaci Ango Ya Saketa Saboda Baya Iya Gamsar Da Ita A Kan Gado

    November 18, 2022

    Yadda Ake Kwalliyar Maida Tsohuwa Yarinya

    November 7, 2022

    Lokuta Da Yawa Maza Yan Iska Sunfi Iya Soyayya Wata Budurwa Ta Kira Ruwa

    November 5, 2022

    Yadda Ango Yayi Dawowar Bazata Ya Kama Matarsa Da Babban Abokinsa Suna Cin Amanarsa

    November 4, 2022

    Bidiyon Hira Da Matar Da Take Auren Maza Biyu Kuma Suke Kwana Kan Gado Daya

    November 3, 2022
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    • About Us
    • Contact Us
    • Disclaimer
    • Privacy Policy
    • Terms & Conditions
    Copyright © 2025 AMIHAD.COM | All Right Reserved.

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.